Nasiru Ado Bayero: Nasaba, Ilimi, Sanaa, Mata, Kudi da Sauran Abubuwa Game da Sarkin Bichi
Me ka sani game da sarkin Bichi na yanzu? Binciken tarihin da Legit.ng Hausa ta yi ya tattaro muku wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan kasaitaccen mai sarauta.
Alhaji Nasiru Ado Bayero shahararren ma'aikacin banki ne, dan kasuwa, kuma sarkin Bichi na yanzu, daya daga cikin garurwa masu daraja a Kano.
An haife shi a ranar 2 ga Fabrairun 1964, kuma da ne ga Alhaji Ado Bayero, wanda ya fi kowa dadewa a kan karagar mulki a masarautar Kano, mahaifiyarsa kuwa Hajiya Maryam Bayero, gimbiya ce daga Ilorin.
Nasiru kani ne ga Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Ado Bayero, kuma kani ga tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, kamar yadda NewsWire ta tattaro.
Bidiyon Bikin Dan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura Da Zukekiyar Amaryarsa Yar Kasar Waje, An Sanya Masa Lalle
Nadin da aka yi masa a matsayin Sarkin Bichi da nadin dan uwansa a matsayin Sarkin Kano, wani tarihi ne da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Masarautar Kano.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nadinsa ya ba da mamaki kasancewar sama da shekaru 1000 da sarautar masarautar ta yi, ba a taba samun ‘yan uwan juna, ciki daya sun yi sarauta a karni guda ba.
A da Nasiru ne Chiroman Masarautar Kano kuma Hakimin Nassarawa kafin a nada shi Sarkin Bichi.
Iliminsa
Nasiru Ado Bayero ya yi karatu jami'ar Maiduguri a shekarar 1987 bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare a Kano inda ya karanta ilimin yada labarai, kamar dai yayansa, Aminu Ado Bayero.
Daga nan ya wuce makarantar kasuwanci ta Harvard da ke Amurka don kara samun takaddun shaida a fannin ilimi.
Nasiru kuma ya samu takardar shaidar iya harshen Jamusanci a 1993.
Buhari: Da zarar an yi kidaya a 2023, za a samu mafita ga matsalar rashin tsaro
Gogewar aikinsa
Nasiru ya yi hidimar kasa na shekara guda a Cibiyar Nazarin Zamantakewa da Tattalin Arziki ta Najeriya (NIER) da ke Ibadan, Jihar Oyo.
Daga baya ya ci gaba da yin aiki da wasu kamfanoni masu yawa, inda ya sami kwarewar aiki a fannin kasuwanci da aikin banki.
Ya yi aiki da Kamfanin Coastal Corporation (Oil and Gas), Houston, Texas; Continental Merchant Bank, Nigeria da Hamlet Investment Inc., da ke a Burtaniya.
Mahaifinsa ya ba shi mukamin Tafidan Kano kuma Hakimin Tarauni yana da shekara 30 a duniya.
A cikin watan Yunin 2000, ya daura rawanin Turakin Kano kuma har ila yau dai Hakimin Tarauni. Amma daga baya an dauke shi daga Tarauni zuwa Nassarawa a watan Mayun 2007 aka nada shi hakimin gundumar.
Daga nan sai aka kara masa mukami zuwa Ciroman Kano sannan ya zama dan majalisar masarautun Kano yayin yake rike da mukamin hakimin gundumar Nassarawa.
Hotunan kafin biki da Kati: 'Dan sarkin Kano, Kabiru Aminu Bayero da Dalleliyar amaryarsa
Aurensa
Jama’a ba su san adadin matan Nasiru Ado Bayero da kuma ‘ya’yansa.
Duk da haka, an san diyarsa, Zahra, ta auri dan shugaban kasa Muhammadu Buhari tilo, Yusuf a shekarar 2021.
Biki ne da ya jawo cece-kuce da jan hankalin jama'a, musamman a kafafen sada zumunta.
Darajar kadararsa
Wata maqalar yanar gizo ta Naija Net Worth ta ba da rahoton cewa dukiyarsa ta kai kusan dala miliyan 15, tare da ikrarin cewa, yana daya daga cikin shugabannin kamfanin sadarwar na 9mobile.
Abubuwan da ya cimma
Mai Martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero mamba ne a jerin shuwagabannin kamfanoni masu tasowa da dama.
Daga ciki akwai kamfanin 9Mobile, SEPLAT Petroleum, Platform Petroleum Limited, Intels (Oilfields) Services Nigeria Limited. Shi shugaba ne a kamfanin mai na Najeriya mai zaman kansa SEPLAT Petroleum (Intels shine babban safarar kan ruwa a Najeriya).
Sauran sun hada da Shugabanci a Kamfanin Enclo Limited, Jami’ar Admiralty ta Najeriya mai hadin gwiwa da rRndunar Sojan Ruwa ta Najeriya da Hellenic Education Nigeria.
Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana
Attajiri Dahiru Mangal: Tarihin Rayuwa, Iyali, Ilimi, Arzikinsa da Sauran Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani
A wani labarin, Dahiru Barau Mangal, fitaccen ɗan kasuwa ne ɗan asalin Najeriya, ya kafa kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air a shekarar 2008, kamar yadda Newwire ta tattaro.
Mangal, mamallakin Max Air, kamfanin sufurin jiragen sama da ke jan ragamar sufuri a cikin gida da ƙasa da ƙasa, ya zuba hannun jari a wasu wuraren da suka haɗa da tafiye-tafiye, Mai da Gas, da gine-gine.
Kasancewarsa Musulmi, Mangal yana da aure kuma Allah ya albarkace shi da samun ƴaƴa da dama. A shekarar 2010 an zargi Attajirin da haihuwa kafin shafa fatiha.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlkbYNyf5hmpZqrmafCbq3DqGSbmamav7B5zZqqmpqRYrattcyiZKyZnpaubrnArZhmo6WZtm6wwGaqmq2ilrturcGuma6vkWK0ornEZpuaZaOWv6y1zWaZopuYnnw%3D